Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta tabbatar da shirin sayen kuraman jirage domin yakin Mali

Ministan tsaron kasar Faransa Jean Yves Le Drian, ya tabbatar da wasu bayanai da ke cewa kasar na shirin sayen jiragen saman yaki maras matuka domin yin amfani da su a kasar Mali.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande REUTERS/Benoit Tessier
Talla

"A yau dai akwai kasashe biyu a duniya da ke kera wadanan jiragen yaki marasa matuka, wato Amurka da kuma Isra’ila, mun riga mun soma tattaunawa da su domin sayen irin wadandan jirage.’’ a cewar ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian wanda ke zantawa da manema labarai a birnin Paris.

Ita dai Faransa ta bayyana aniyarta ta sayen irin jiragen guda biyu samfurin Reaper daga Amurka, domin yin amfani da su a yakin da ta ke yi da ‘yan tawayen kasar Mali, kuma Amurka za ta bai wa Faransa jiragen kafin karshen wannan shekara ta 2013.

Lokacin da aka tambayi Jean Yves Le Drian sanin hakikannin adadin jiragen da kasarsa ke shirin saye daga Amurka ko kuma Isra’ail, sai ya kada baki ya ce akalla daya, to sai dai wasu bayanai sun ce ma’aikatar tsaron Faransa na shirin sayen akalla 12 ne, duk da cewa wasu daga cikinsu na sintiri ne ba wai yaki ba.

Duk da matsayinta a siyasar kasa da kasa da kuma gogewarta a bangaren kimiya, har yanzu Faransa, ba ta kera jiragen yaki marasa matuka wadanda ake tinkaho da su a yau a duniya, abin da ministan ya ce wani abin assha ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.