Isa ga babban shafi
Syria-Geneva

‘Yan adawar Syria suna nan kan bakarsu a taron Geneva

‘Yan adawar kasar Syria sun jajirce lalle sai shugaba Bashar Al Assad ya yi murabus a yayin da wakilan bangarorin biyu ke zaman taron sasantawa a Geneva. A wani matakin sulhu da aka cim ma Majalisar Dinkin Duniya tace Syria ta amince mata da kananan yara su fice daga garin Homs da aka yi wa kawanya.

'Yan adawar kasar Syria suna zanga-zanga a harabar ginin Majalisar Dinkin Duniya a Geneva inda ake zaman sasantawa da gwamnatin Bashar al Assad da 'Yan adawa
'Yan adawar kasar Syria suna zanga-zanga a harabar ginin Majalisar Dinkin Duniya a Geneva inda ake zaman sasantawa da gwamnatin Bashar al Assad da 'Yan adawa REUTERS/Jamal Saidi
Talla

Zaman taron sasanta rikicin kasar Syria da aka gudanar a kwanaki biyu ya mayar da hankali ne akan batun da ya shafi agaji ga mutanen Syria. Gwamnatin Syria ta yi watsi da duk wani mataki na kawar da gwamnatin Bashar Al-Assad daga saman mulki.

Mai shiga tsakani don sasanta rikicin kasar, Lakhdar Brahimi yace an samu ci gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu saboda dukkaninsu suna mutunta juna.

Mataki na farko da aka cim ma a zaman sulhun shi ne amincewa da Gwamnatin Assad ta yi na ba yara da mata damar ficewa daga yankunan da Mayaka suka mamaye a garin Homs.

A zaman tattaunawar da za’a soma a yau Litinin ‘Yan adawa sun ce yanzu lokaci ya yi da za a tabo batun shugabanci.

Zaman sasantawar ya kunshi jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da Rasha da Amurka wadanda ke fatar samun maslaha a zaman taron domin kawo karshen zubar da jini a kasar Syria da aka kwashe kusan shekaru uku ana yaki.

Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun ce sama da mutane dubu dari da talatin ne suka mutu tun barkewar rikicin a watan Maris na 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.