Isa ga babban shafi
Syria-Geneva

Babu haske a taron sasanta rikicin Syria a Montreux

Babban mai shiga tsakanin rikicin Syria Lakhdar Brahimi zai kebe tare da wakilan bangarorin da ke rikici a Syria bayan sun yi musayar kalamai a zaman farko na taron sasanta rikicin kasar da ya lakume rayukan daruruwan mutane. Manyan kasashen duniya suna fatar a yi zaman gaba da gaba ne tsakanin ‘Yan adawa da wakilan Gwamnatin Assad domin kawo karshen zubar da jini.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya  Ban Ki-moon tare da Lakhdar Brahimi a zaman taron sasanta rikicin Syria a Montreux
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon tare da Lakhdar Brahimi a zaman taron sasanta rikicin Syria a Montreux REUTERS/Gary Cameron
Talla

Babban muradin taron da aka bude a Montreux shi ne makomar Shugaban Syria Bashar al Assad.

Babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon da ke jagorantar taron, yace lokaci ya yi da al’ummar kasar Syria za su aje makamansu, don tattaunawa da zummar samo maslahar magance rikicin kasar.

Yayin da ya ke gabatar da jawabi a jiya Laraba, Mr Ban ya bayyana fatar ganin taron ya amince da kafa gwamnatin rikon kwarya mai cikakken iko.

Tuni dai Iran tace babu maslahar da za’a cim ma a taron saboda akwai bangarorin da ke goyon bayan ‘Yan tawaye cikin kasashen duniya da ke jagorantar zaman taron.

Amma masana diflomasiya suna ganin zaunawa a teburin sulhu tsakanin ‘Yan adawa da Bashar al Assad mataki ne mai inganci da zai iya kai wa ga shawo kan rikicin kasar Syria.

Dukkanin bangarorin biyu dai sun jajirce akan bukatunsu, inda Shugaba Assad yace ba zai sauka akan mukamin shi na shugaban kasa ba kamar yadda ‘Yan adawa suka bukata.

Ministan harakokin wajen Syria Walidi Mu’allem wanda ke jagorantar tawagar gwamnati a taron na birnin Montreux, yace al’ummar kasar ce ke da hurumin daukar mataki akan mokomar kasarsu.

Jagoran tawagar ‘yan adawan Syria Ahmad Jarba, yace sun zo taron ne domin neman kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya da zata maye gurbin Shugaba Assad.

A watan Maris na 2011 rikicin Syria ya barke bayan kaddamar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Bashar al Assad kamar yadda ta faru a kasashen Tunisia da Masar da Libya da Yemen.

Yanzu haka rikicin Syria ya rikide zuwa yakin basasa inda akwai mayaka da dama da suka shiga yaki a kasar.

Mutane sama da dubu dari ne Majalisar Dinkin Duniya tace sun mutu a rikicin Syria yayin da daruruwa suka fice kasar domin tsira da ransu zuwa makwabtan kasashe.

A cikin wani sakon Bidiyo, shugaban Kungiyar Al Qaeda Ayman al-Zawahiri ya yi kira ga mayakan Jihadi su dai na kashe kansu da sunan yaki a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.