Isa ga babban shafi
Syria-Geneva

An soke gayyatar da aka yi wa Iran zuwa taron Geneva

Majalisar Dinkin Duniya ta soke gayyatar da ta yi wa kasar Iran domin ta halarci taron sasanta rikicin kasar Syria da za’ayi gobe a garin Montreux na kusa da Geneva a kasar Switzerland.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya
Talla

Mai Magana da yawun Majalisar Martin Nesirky, ya soki matsayin Iran na kin amincewa da shirin kafa gwamnatin rikon kwarya a Syria da kasahsen duniya ke shirin yi a lokacin wannan taro.

Tun da farko dai kasashen Yammacin duniya sun yi Allah wadai da gayyatar da Ban ki Moon ya yi wa Iran na halartar taron, inda suka bukaci Iran da ta kawo karshen adawa da shirin kafa sabuwar gwamnatin rikon a Syria, kafin barin ta ta halarci taron, abinda Iran ta ce ba za ta amince da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.