Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Brahimi ya yi tattaunawar sirri da 'yan tawayen Syria

Mai shiga tsakani kan rikicin kasar Syriya Lakhdar Brahimi, ya yi wata ganawar siri da shuwagabannin ‘yan tawayen kasar Syriya, domin shawo kansu su halarci babban zaman taron warware rikicin kasar Syriya da za a fara a yau juma'a a birnin Geneva na kasar Switzerland. Ganawar farko ta ranar larabar da ta gabata tsakanin wakilan shugaban kasar Syriya Bashar Al’Assad da na ‘yan adawar kasar dake gudun hijira, da aka yi a gaban wakilan kasashen duniya 40, ta tashi baram baram babu wanda ya fahimci wani, ta hanyar jifar juna da bakaken kalamai zargi da kuma cin amana.Sai dai kuma a yau juma a ne, a birnin Janiva mai shiga tsakani na kasarshen duniya da Majalisar Dinkin Duniya Lakhdar Barahimi, zai yi ganawar keke da keke da wakilan bangarorin 2, inda zasu shiga cikin gundarin maudu’in sasantawar.Tun Ministan harakokin wajen kasar Rasha Sergui Lavrov ya bayyana tattaunawar da cewa ba mai sauki bace balantana a yi mata gaggawa.Wasu manazarta lamuran na ganin tattaunawar a matsayin zaman shan shayi, ganin irin yadda bangarorin 2 keta gidaya sharrudan da mawuyacin abune daya bangaren ya amince da su, ga kuma bangaren magoya baya, irin su Amruka Fransa, saudiya da kuma Taki, dake nuna goyon bayan su ga ‘yan tawaye, a yayinda a dai bangaren kuma Rasha Iran da China ke ci gaba da dafawa gwamnatin Bashar al’Assad baya. 

Mai shiga tsakani a rikicin kasar Siriya Lakhdar Brahimi
Mai shiga tsakani a rikicin kasar Siriya Lakhdar Brahimi REUTERS/Arnd Wiegmann
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.