Isa ga babban shafi
Syria

Brahimi ya tattauna da Shugaba Bashar al -Assad

Lakhdar Brahimi ya ce ganawarsu da shugaban kasar Syria, Bashar al Assad ta ba su damar tattaunawa dangane da halin da ake ciki a kasar ta Siriya, yana mai cewa ko shakka babu rikicin da ake fama da shi a kasar kusan a kowace rana sai dada tsananta ya ke, Sai dai ya ce har yanzu yana cike da fatar ganin dukkanin bangarorin da ke da hannu a wannan rikici sun shiga tattaunawa da nufin warware sabanin da ke tsakaninsu.  

Lakhdar Brahimi tare da Shugaban kasar Syria, Bashar al- Assad
Lakhdar Brahimi tare da Shugaban kasar Syria, Bashar al- Assad REUTERS/Sana
Talla

Manzon na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yakin da ake fama da shi a Syria ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu 44, kuma kokarin kawo karshensa ne babban dalilin yin ganawa da shugaba kasar.

Brahimi ya ce shugaba Assad ya bayyana mai matsayinsa a game da wannan hali, inda ya kara da cewa ya sanar da shi irin shawarwarin da muka yi da shugabannin kasashen yankin da kuma sauran wadanda ke da hannu a wannan batu.

A baya-bayan nan dai manzon na Majalisar Dinin Duniya, kan rikicin na Syria ya gana a lokuta daban-daban da manyan Jami’an kasar Amurka da kuma na Rasha, to sai dai kamar kullum har yanzu akwai bambancin ra’ayi a tsakanin kasashen biyu kan yadda za a tunkari rikicin na Siriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.