Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

Kotun sauraron kararrakin zabe ta kori karar Atiku kan zaben 2019

Kotun sauraron kararrakin zabe a Najeriya, ta kori karar dan takarar neman kujerar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar bayan da ta tabbatar da nasarar shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari a zaben kasar na watan Fabarairun da ya gabata.

Zaman karkare shari'ar zaben Najeriya a kotun sauraron kararrakin zabe da ke Abuja yau Laraba 11 ga watan Satumba 2019.
Zaman karkare shari'ar zaben Najeriya a kotun sauraron kararrakin zabe da ke Abuja yau Laraba 11 ga watan Satumba 2019. Channels TV
Talla

Shari’ar wadda ta gudana karkashin jagorancin lauyoyin kotun 5 baya ga korar karar ta Atiku Abubakar da PDP ta kuma wanke dan takarar daga zargin kasancewar dan kasar Kamaru.

Haka zalika zaman karkare sauraron shari’ar a yau Laraba, ya kuma yi watsi da zargin amfani da Soji baya ga ‘yan sanda wajen tafka magudi a zaben kasar da ya gudana.

Bugu da kari zaman shari’ar na yau, ya kuma wanke shugaban kasar Muhammadu Buhari daga zargin rashin takaddun shaidar kammala karatun Sakandire.

Yayin zaman sauraron shari’ar kotun sauraron kararrkin zaben ta kuma wanke zargin da ke cewa rumbun adana bayanai na hukumar zaben Najeriyar INEC ya bayyana Atiku Abubakar a matsayin wanda ya yi nasara a zaben na watan Fabarairu.

Da ya ke karanta hukuncin Kotun Garba Mohammed ya ce Muhammadu Buhari mai shekaru 76 shi ne ya yi nasara a zaben karkashin Jam’iyyar APC yayinda Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDB da ke matsayin babbar Jam’iyyar adawa ke biye masa baya a matsayin na biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.