Isa ga babban shafi
Najeriya

Na'urar Card reader ce ta taimaka min na lashe zaben 2015- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana yadda katin tantance masu kada kuri’u da ake kira ‘Card Reader’ ya taka gagarumar rawa wajen taimaka masa samun nasarar zaben shekarar 2015.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ng.gov.jpg
Talla

A wata hira ta musamman da ya yi da Jaridar Premium Times, Buhari ya ce abu ne mai wuya wadanda basa cikin gwamnati su lashe zabe, saboda yadda shugabannin da ke karagar mulki ke gudanar da magudin zabe domin bai wa wadanda suke so damar hawa karagar mulki wajen rubuta alkaluman karya.

Shugaban ya ce amfani da katin tantance masu kada kuri’un ya taimaka wajen bai wa jama’a damar zabin abinda su ke so da kuma tabbatar da ganin an kaucewa yin magudi.

Buhari ya bayyana cewar zai mayar da hankalin sa wajen kirkiro ayyukan yi ga matasa da samar da wutar lantarki da tabbatar da tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa a sabon wa’adin da ya fara.

Haka zalika Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen sake manhajan ilimin kasa baki daya wanda zai karkata zuwa bangaren kimiya da fasaha, yayin da za su cigaba da tallafawa marasa karfi da kudade tare da kananan yan kasuwa da matasa da kuma mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.