Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC ta hada baki da gwamnati don tafka magudi inji PDP

Jam’iyyar PDP na zargin hukumar zaben Najeriya INEC da hada baki da gwamnati da kuma wasu manyan jami’an tsaron kasar don shirya magudi a zaben da za a sake yi ranar asabar a wasu jihohin kasar,

Pr Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta
Pr Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images
Talla

Sakataren yada labaran jam’iyyar ta PDP Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa tuni wasu manyan jami’an hukumar zaben suka gudanar da taro da takwarorinsu na fadar shugaban kasa da kuma jami’an tsaro domin shirya yadda za a kwace nasarar da ‘yan takarar jam’iyyar za su yi a zaben na ranar asabar.

Hukumar INEC ta ce tabbas jami’anta sun gana da manyan jami’an tsaron kasar, to amma wannan taro ne da ake yi lokaci zuwa lokaci don tabbatar da tsaro a lokacin zabe.

Sakataren yada labaran PDP Mr Ologbondiyan ya ce a dukkanin jihohin da ya kamata a sake zaben, ‘yan takararsu ne ke sahun gaba, abin da ke tabbatar da cewa

Hukumar zaben ta yanke shawarar sake gudanar da zaben gwamnoni a wasu mazabu da ke jihohi 6 da suka hada da Adamawa, Benue, Sokoto, Plateau, Kano da kuma Bauchi sakamakon kura-kuran da aka samu a zaben ranar 9 ga watan maris, to sai dai ga alama ba za sake zaben a wasu daga cikin jihohin musamman Adamawa saboda umurnin kotu.

PDP dai ta ce tana da cikakkun bayanan da ke tabbatar da cewa ana son yin amfani da jami’an tsaro don kwace ma ta nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.