Isa ga babban shafi
Najeriya - Kano

Zaben kujerar Gwamnan jihar Kano bai kammala ba - INEC

Hukumar zaben Najeriya Najeriya INEC ta bayyana zaben kujerar Gwamnan jihar Kano da ya gudana a ranar Asabar 9 ga watan Maris, a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Kano State Government
Talla

Shugaban hukumar zaben na jihar Kano Farfesa Bello Shehu ne ya sanar da halin da ake ciki kan zaben Gwamnan da yammacin ranar Litinin.

Farfesa Shehu, ya ce sakamakon da suka tattara ya nuna cewa dan takarar jam’iyyar PDP Abba Yusuf ya samu kuri’u miliyan 1, da dubu 14, da 474, yayin da Gwamna mai ci na jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri’u dubu 987 da 819.

Farfesa Shehu ya kara da cewa, an samu tazarar kuri’u dubu 26 da 655 tsakanin Abba da Ganduje, sai dai kuma, yawan kuri’un da aka soke a kananan hukumomin jihar ta Kano 22, ya kai dubu 141, da 694, hakan tasa tilas a sake gudanar da zaben Gwamnan a inda aka soke kuri’un, la’akari da cewa yawansu zai iya tasiri wajen tabbatar da nasarar wanda ke kan gaba, ko sauya sakamakon zaben.

A halin yanzu dai Kano ta bi sahun jihohi da zaben kujerunsu na Gwamna bai kammala ba, da suka hada da Benue, Filato, Adamawa, Bauchi da kuma Sokoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.