Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Dattijai ta nemi sanya dokar ta baci a jihohin da ake rikici

Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa ya kafa dokar ta baci a Jihohin Beneu da Taraba da Nasarawa da Zamfara saboda cigaba da kashe kashen da ake samu a cikin su.

Majalisar Dattijan Najeriya.
Majalisar Dattijan Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Wannan ya biyo bayan Karin kashe kashen da aka samu a Jihar Benue da ake dangantawa da kisan daukar fan sa da Yan kabilar Tibi suka kai, bayan kasha wasu limaman Kirista da magoya bayan su.

Yayin tafka mahawara kan kisan da aka samu na baya bayan nan a Jihar Benue wanda ya ritsa da wani mai bushara da mabiyan sa, Yan Majalisar Dattawan sun ce sun gaji da tsayuwar da suke don nuna alhini kan kisan, inda suka bukaci gwamnati ta dauki tsauraran matakai.

Sanata Mao Ohagbunwa ya ce yana goyan bayan kudirin kafa dokar ta baci a Jihohin da ake samun rikicin, yayinda Sanata Victor Umeh ya ce babu wanda zai ce Najeriya ba ta da dakarun da za su iya magance wannan matsala.

Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Sanata Godswill Akpabio ya ce yan majalisun su jingine batun jam’iyya domin shawo kan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.