Isa ga babban shafi
Najeriya

Wasikar Buhari ta janyo muhawara a zauren majalisar dattijai

A yau Talata shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki, ya karantawa zauren majalisar wasikar da shugaban kasar Muhammadu  Buhari ya aike masu kan sake komawa birnin London domin a duba lafiyarsa.

Zauren majalisar dattijjan Najeriya.
Zauren majalisar dattijjan Najeriya. venturesafrica
Talla

To sai dai karanta wasikar ke da wuya muhawara ta barke tsakanin ‘yan majalisar, bisa abinda wasunsu suka kira da rashin bayyana mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da Buharin bai yi ba a matsayin mukaddashin shugaban kasa, a fayyace.

Cikin wasikar dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ambata cewa babu kayyadajjen lokacin da zai dawo gida, dan haka mataimakinsa farfesa Osinbajo zai cigaba da kula da al’amuran tafiyar da gwamnatin kasar, kamar yadda sashi na 145 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada dama.

Al’amarin da ya janyo kace-nace tsakanin wadanda ke ganin kamata yayi ace shugaban ya fito fili wajen ambata Farfesa Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

Wasu masharhanta na kallon kalamin da shugaba Buhari yayi amfani da shi cikin wasikar a matsayin wanda bai kamata a ce ana ta cece kuce kansa ba, kasancewar kalamin na nuna cewa mataimakin nasa ne zai cigaba da jagorancin shugabancin kasar, har zuwa lokacin da zai dawo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.