Isa ga babban shafi
Najeriya

An kara samun arangama tsakanin mabiya Shi'a da jami'an tsaro a Najeriya

An kara samun arangama tsakanin mabiya Shi’a da jami’an ‘Yansanda a Abuja babban birnin Najeriya, bayan wata zanga-zanga da suka kara gudanarwa yau don neman sakin jagoransu Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky.

A baya-bayan nan ne dai Zakzaky ya fito ya shaidawa mabiyansa cewa yana cikin koshin lafiya.
A baya-bayan nan ne dai Zakzaky ya fito ya shaidawa mabiyansa cewa yana cikin koshin lafiya. AFP PHOTO PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Wanann dai shi ne karo na biyu da mabiya Shi’an suka gudanar da zanga-zanga cikin kasa da kwana goma inda a ranar 16 ga watan Aprilu jami’an ‘yansanda suka kame akalla mabiyan 15 bayan zanga-zangar da ta kai ga barnata kadadrorin jama’a da na gwamnati.

Jami'an tsaron sun yi amfani da karfin tuwo don tarwatsa masu zanga-zangar kamar yadda ya faru a makon jiya inda aka yi amfani da hayaki mai sanya hawaye don tarwatsa su.

Hukumomin kare hakkin dan adam dai na ganin gwamnatin Najeriyar ta ki mutunta umarnin da aka bata na sakin Sheikh Ibrahim Zakzaky, ko da ya ke dai tana ikirarin cewa tana kare lafiyarsa ne la'akari da cewa rayuwarsa na cikin hadari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.