Zanga-zangar yan Shi'a a Abuja
Yan sanda a Najeriya sun yi amfani da karfi tare da barazanar harbi don tarwatsa taron mabiya mazhabar Shi’a da ke gudanar da zanga-zanga yau a babban birnin kasar Abuja.
Wallafawa ranar:
Dandazon mabiya Shi’ar na bukatar ganin gwamnatin kasar ta bi umarnin kotu wajen sakin jagoransu Sheikh Ibrahim Zazzaki da take rike da shi kusan shekaru biyu.
Masana kan harkokin shari’a a tarayyar Najeriya, na bayyana matakin a matsayin abinda ke kara zama barazana ga zaman lafiyar kasar.
Gwamnatin Najeriya na tsare da shugaban kungiyar ta IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, tun bayan arrangamar da sojoji suka yi da mabiyansa a shekarar 2016, duk da umurnin da wata kotu a Abuja ta bayar na cewa a saki shugaban na IMN da matarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu