Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Winnie Mandela matar tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela ta mutu

Winnie Mandela, tsohuwar matar tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu marigayi Nelson Mandela, ta mutu a yau litanin 2 ga watan Afrilu 2018, tana yar shekaru 81 a duniya. sakamakon fama da doguwar rashin lafiya da ta yi a wani asibiti dake Johannesburg, kamar yadda kakakinta ya sanar.

Winnie Mandela a watan désemba 2017 a wajen taron jam'iyar ANC karo na  54e  a Johannesburg.
Winnie Mandela a watan désemba 2017 a wajen taron jam'iyar ANC karo na 54e a Johannesburg. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Nomzamo Winifred Zan-yiwe Winnie Madikizela-Mandela, matar da aka fi sani da Winnie Mandela, ta kasance yar siyasar kasar Afrika ta kudu, mamba a jamíyar l'ANC mai mulkin kasar, an haifeta ne a ranar 26 septembre 1936 Bizana kasar Afrika ta kudu kafin ta koma ga mahalicinta Allah a yau 2 ga watan Afrilun 20181.

Ta zama mata ta 2 ga tsohon shugaban Afrika ta kudu dottijo marigayi Nelson Mandela daga 1958 zuwa 1996, kafin aurensu ya mutu. Bisa umarnin mijinta Nelson mandela wanda ta haifawa yaya 4 Zoleka Mandela, Zondwa Mandela, Bambatha Mandela, Zwelabo Mandela-Hlongwane

Winnie Mandela, daya daga cikin fuskokin yan gwagwarmayar nuna kyamar wariyar launin fata na tsawon shekaru 25, ta kasance mace da a kullum ke tsaye cikin gwagwarmayar siyasar kasar.

Winnie Mandela na daya daga cikin takwarorinta yan gwagwrmaya da suka ci kason turawan mulkin wariyar jinsi na Apartheid tsakanin 1969 zuwa1970.

Kafin mutuwarta Wini ta kafa wata jarida dake wallafa wasikun da ita da mijinta suka rubutawa juna a gidajen kaso da ake tsare dasu kafin a sallameta bayan share tsawon shekaru 7 a daure

A lokacin da take kaddamar da littafinta da ta rubuta mai sunan kwanaki 421 na zaman wakafi, dan kaso mai lamba 1323/69", tace ta yanke shawarar rubuta littafi ne domin tbarin tarihi ga matasa sabin tashi, hakan kuma zai taimaka wajen kaucewa sake faruwar mummunan bakin mulkin wariyar launin fatar da kasar Afrika ta kudu ta tsinci kanta a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.