Isa ga babban shafi
Afrika

'Yan fashi sun saki jirgin da suka yi garkuwa da shi a Tekun Guinea

‘Yan fashin teku a gabar tekun Guinea sun sako jirgin ruwan da suka yi garkuwa da shi mai dauke da gas tan dubu 13 da dari biyar baya ga ma’aikatansa ‘yan indiya 22. Rahotanni sun ce dukkanin ma’aikatan jirgin lafiyarsu kalau haka zalika jirgin dama dukiyar da ke cikinsa.

Rahotanni sun ce dukkanin ma’aikatan jirgin lafiyarsu kalau haka zalika jirgin dama dukiyar da ke cikinsa.
Rahotanni sun ce dukkanin ma’aikatan jirgin lafiyarsu kalau haka zalika jirgin dama dukiyar da ke cikinsa. Matthew Kay
Talla

Tun a juma’ar da ta gabata ne ‘yan fashin suka yi garkuwa da jirgin wanda aka yi  Maganar karshe da jami’ansa a dai dai lokacin da suka isa Benin amma daga bisani aka rasa inda jirgin ya shiga.

Tekun na Guinea a baya-bayan nan ya zamo babbar maboyar ‘yan fashi ta yadda suke yin garkuwa da manyan jiragen dakon kaya tare da bukatar kudin fansa.

Wani rahoto da hukumar sanya idanu kan sufurin ruwa ta duniya IMB ta fitar ya nuna cewa fashin teku na ci gaba da tsananta a tekun na Guinea tun daga bara, yayinda yake neman zama babbar barazana a tsaron ruwa na yankin yammcin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.