Isa ga babban shafi
Kenya

Kenya ta kafa doka mai tsauri kan haramcin amfani da leda

Gwamnatin kasar Kenya ta haramta amfani da jakar daukar kaya ta leda, tare da gargadin duk wanda aka samu yana saidawa ko amfani da jakar zai gamu da hukuncin daurin shekaru 4 ko biyan tarar Dala 40,000.

Wasu jakunkuna na ledoji da aka yasar a Kenya.
Wasu jakunkuna na ledoji da aka yasar a Kenya. Africa Review
Talla

Matakin ya sanya kasar cikin jerin kasashe 40, daga cikinsu akwai China, Faransa, Rwanda da Italia, da suka haramta amfani da jakar leda.

Ministar muhallin Kenya, Judy Wakhungu, tace dokar ta baiwa ‘yan sanda damar kama duk wanda aka samu da laifi.

Sai dai da alama matakin bai yi wa masu masana’antu dadi ba, inda kakakin su Samuel Matonda, yace akalla mutane 60,000 zasu rasa ayyukansu daga kamfanoni 176 da dokar ta tilasta rufe su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.