Isa ga babban shafi
Kenya

Likitocin Kenya sun yi barazanar tilastawa asibitoci masu zaman kansu

Likitocin Kenya dake yajin aikin da ya durkusar da ayyukan kula da lafiya a fadin kasar, sun yi barazanar tilastawa asibitoci masu zaman kansu a makon gobe, muddin gwamnatin kasar ta kasa biya musu bukatun su.

Likitoci da ke yajin aiki a Kenya
Likitoci da ke yajin aiki a Kenya
Talla

Yanzu haka an kwashe kwanaki 5 asibitocin kasar na rufe, yayin da marasa lafiya suka shiga cikin halin tasku, inda wasu suka koma gida, masu karfi kuma suka koma asibitoci masu zaman kan su.

Kungiyar likitocin na bukatar Karin kashi 300 na albashi, da kuma karin kashi 40 ga masu taimaka musu, a karkashin yarjejeniyar da suka kulla da gwamnati a shekarar 2013.

Sai dai kuma gwamnatin Kenya ta bukaci ragi kan alkwarin baya amma likitocin suka ce basu san zancen ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.