Gambia ta kafa kwamitin da zai binciki kadarorin Jammeh
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya kafa wani kwamiti na musamman, da ya dorawa alhakin bincikar yadda tsohon shugaban kasar Yahya jammeh ya tafiyar da gwamnatinsa, da kuma kadarorin da ya mallaka.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kwamitin, zai binciki fannonin da suka hada da kwangilolin da gwamnatin Jammeh ta aiwatar, yadda gwamnatin ta sarrafa kudaden kasar, kadarorin da ya mallaka da kuma wadanda iyalai da mukarrbansa suka mallaka yayin zamanin gwamnatin ta Jammeh.
A watan Mayun da ya gabata gwamnatin Adama Barrow ta kwace kadarorin Yahya Jammeh, da aka kiyasta cewar darajarsu zata kai akalla dala miliyan 50, tare da rufe asusun ajiyar bankuna tamanin da ke da alaka da tsohon shugaban kasar.
A halin yanzu Jammeh yana gudun hijira a kasar Equatorial Guinea, sakamakon kayen da ya sha a zaben watan Disambar bara, bayan shafe shekaru 22 da biyu yana mulkin Gambia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu