Isa ga babban shafi
Chadi

Mutane miliyan na bukatar tallafi a tafkin Chadi

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar akalla mutane kusan miliyan guda ne rikicin Book Haram ya katse hanyar da za a kai musu tallafi a Yankin tafkin Chadi duk da kokarin sojojin kasashe biyar da ke yaki da mayakan kungiyar.

Rikicin Boko Haram ya toshe kafar shigar da kayan tallafi ga mutanen tafkin Chadi
Rikicin Boko Haram ya toshe kafar shigar da kayan tallafi ga mutanen tafkin Chadi © HCR/M. Farman Farmaian
Talla

Babban jami’in agaji na Majalisar Dinkin Duniya Toby Lanzer wanda ya ziyarci kasashen da rikicin Boko Haram ya shafa a kwanakin baya, ya ce duk da nasarorin da jami’an tsaro ke samu wajen kubutar da garuruwa daga hannun mayakan, har yanzu akwai yankunan da ba a zuwa wanda hakan ya sa ba a iya kai musu agajin da suke bukata ba.

Mista Lanzer ya ce har yanzu hankalinsu ba a kwance ya ke ba dangane da yanayin tsaro a Yankunan da ke fuskantar rikicin Boko Haram ganin yadda mayakan ke ci gaba da kisan mummukeda sari ka noke.

Majiyar jami’an tsaro ta ce yanzu haka sojoji na kokarin kakkabe mayakan kusa da tafkin Chadi domin ganin mutanen yankin sun koma sana’ar su ta noma

A makon jiya daruruwan mayakan suka mika kan su ga jami’an tsaro a kasar Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.