Isa ga babban shafi
Egypt

An tsamo jirgin ruwan da ya nitse da 'yan cirani 450

Hukumomin Kasar Masar sun ce sun yi nasarar tsamo jirgin ruwan nan da ya nitse da baki 450 a teku, tare da karin wasu gawawaki 33, abinda ya kawo adadin gawawakin da aka samu zuwa 202.

An gano gawarwakin 'yan cirani 202 daga teku bayan hadarin da ya rusta dasu.
An gano gawarwakin 'yan cirani 202 daga teku bayan hadarin da ya rusta dasu. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Rundunar sojin kasar ta tabbatar da ceto bakin 163 abinda ke nuna cewar bakin dake cikin jirgin sun zarce 365.

An dai kama mai kwale kwalen da wasu ma’aikatan sa guda uku da za’a gurfanar da su a gaban kotu.

Wasu da suka tsallake rijiya da baya a hadarin, sun ce akalla baki 450 suke cikin jirgin kamun kifin lokacin da yayi hadari akan hanyar sa ta zuwa Italia daga Masar.

Bayanai sun ce jirgin ya nitse ne kusa da tashar jiragen ruwan Rosetta.

Cikin wadanda suka mutu harda mata da yara kanana, da akasarinsu sun fito ne daga Masar, Habasha, Sudan da Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.