Isa ga babban shafi
Masar

An kama bakin haure kusan 230 da suka tashi daga Masar zuwa Turai

Rundunar sojan ruwan kasar Masar tace ta kama wani kwale kwalen kamun kifi guda 3, dauke da bakin haure kusan 230, da ma’aikata 17, a kan tekun Meditereniya.

wani kwale kwale dauke da bakin haure
wani kwale kwale dauke da bakin haure Reuters/Reuters
Talla

Sanarwar da rundunar sojan kasar ta fitar tace bincike ya nuna cewa mutanen dake cikin kwale kwalen sun fito ne daga kasashe daban daban, da kuma ke kokarin tsallakawa ta Masar din.
Sanarwar bata bayyana kasashen da mutanen suka fito ba, sai dai tace an kaisu sansanin sojan ruwan kasar, dake birnin Alexandria.
A kwanakin nan ana samun matsalar kwararar bakin haure daga nahiyar Afrika da Asiya zuwa wasu kasashen nahiyar Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.