‘Yan fashi sun karkatar da jirgin Masar zuwa Cyprus
‘Yan sandan Cyprus sun ce Jirgin EgyptAir na kasar Masar da wasu ‘yan fashi da ba a tantance ba suka karkatar ya sauka a filin jirgin Larnaca kudancin kasar a yau Talata. Yanzu haka an baza jami’an tsaro a filin jirgin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotanni sun ce wani dan bindiga ne guda ya kwace ikon jirgin mai dauke da fasinja kimanin 80 akan hanyarsu daga birnin Alexandria zuwa Al Kahira.
‘Yan sandan Cyprus sun ce Maharin ya nemi izinin sauka filin jirgin Larnaca da safiyar yau Talata. Zuwa yanzu babu wani cikakken bayani akan dalilin sace jirgin.
Rahotanni sun ce dan bindigar ya ba fasinjojin da ke cikin jirgin ficewa amma tare da yin garkuwa da wasu Turawa 5 bayan sun sauka a Larnaca.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu