Isa ga babban shafi
Rasha

Masu bincike sun yi amannar bom ne ya tarwatse jirgin Rasha

Kashi 90 cikin dari na Masu binciken hatsarin jirgin saman Rasha da ya kashe mutane 224 a sararin samaniyar kasar Masar, sun yi amannar cewa bam ne ya yi sanadiyyar fadowar jirgin a yankin Sinai.

Jirgin Fasinjan Rasha da ya tarwatse a yankin Sinai na Masar
Jirgin Fasinjan Rasha da ya tarwatse a yankin Sinai na Masar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Masu binciken sun ce akwai kara mai kama da fashewar bom da aka ji daga na’urar da ke nadar bayanai a jirgin.

Jirgin dai ya tarwatse ne bayan tashinsa minti 23 daga tashar Sharm al Sheikh a Masar a ranar Asabar karshen makon jiya. Kuma tuni mayakan IS da ke da’awar jihadi suka yi ikirarin daukar alhakin tarwatsewar jirgin.

Hasashen da ake bom ne ya tarwatse jirgin, ya sa baki ‘yan yawon bude na gaggawar ficewa Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.