Isa ga babban shafi
Masar

IS ta yi ikirarin kai hari kan 'yan sandan Masar

Kungiyar IS ta dau alhakin harin kunar bakin wake kan jami’an 'yan sandan Masar a yankin Sinai, inda ta kashe akalla ‘yan sanda uku.

Kungiyar IS ta yi ikirarin kaddamar da harin kan 'yan sandan Masar.
Kungiyar IS ta yi ikirarin kaddamar da harin kan 'yan sandan Masar. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Kafar talabijin ta kasar ta bayyana cewa akwai wadanda suka jikkata sakamakon harin wanda aka kaddamar da mota makare da bama bamai kuma IS ta ce wani mambanta ne ya tuka motar.

Mayakan IS dai sun kaddamar da jerin hare hare a yankin Sinai a ‘yan watannin da suka shude duk da shirin sojojin masar na kokarin kakkabe masu tayar da kayar baya a yankin na Sinai mai iyaka da kasar Isra’ila da zirin Gaza.

Sabon harin na yau, na zuwa ne kwanaki kalilan da kungiyar ta yi ikirarin kakkabo jirgin fasinjan Rasha dauke da mutane 224.

To sai dai hukumomin Masar da Rasha sun yi watsi da ikirarin kungiyar yayin da hukumar leken asiri ta Amurka ta ce hatsarin ba shi da nasaba da aikin ta’addanci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.