Isa ga babban shafi
Djibouti

A na zaben Shugaban kasa a Djibouti

Al’ummar Djibouti na gudanar da zaben shugaban kasa inda ake sa ran shugaba mai ci Ismail Omar Guelleh zai lashe duk da ya shafe shekaru 17 yana jagorantar karamar kasar da manyan kasashen duniya suka sa wa ido.

Shugaban kasar Djibouti Ismaïl Omar Guelleh
Shugaban kasar Djibouti Ismaïl Omar Guelleh AFP/Jim Watson
Talla

Tun dai da misalin karfe 6 na safe ne aka bude runfunan zabe a kasar.

‘Yan takara shida ne ke neman kujerar shugaban kasa a zaben na Djibouti, kuma daga cikin yan takarar akwai shugaba Guelleh da ke neman wa’adin shugabanci na hudu bayan ya karbi mulki daga dan uwansa Hassan Aptidon da ya jagoranci kasar tun loakcin samun ‘yanci a 1977 zuwa 1999.

Mutanen kasar kimanin dubu 187 ke da ‘yancin kada kuri’a a zaben daga cikin yawan jama’ar kasar dubu 875.

Manyan masu hammaya da shugaban kasar sun hada da Mohammed Daoud Chahem da Omar Elmi Khaireh

Sai dai kuma wasu jam’iyyun adawa sun kaurace.

‘Yan adawar sun yi korafin cewa an janye wakilansu a wasu runfunan zaben tare da bayyana shakku ga sahihancin zaben da ake gudanarwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.