Isa ga babban shafi
Spain

Barcelona za ta bude makarantar kwallo a Lagos

Tawagar  Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta kasar Spain sun isa birnin Lagos  dake Najeriya da labarin bude makarantar horas da ‘yan wasan kwallon kafa.

Lionel Messi da Neymar, 'yan wasan Barcelona
Lionel Messi da Neymar, 'yan wasan Barcelona REUTERS
Talla

Gwamnan jahar Lagos Akinwumi Ambode ne ya karbi tawagar a ofishin sa dake Alausa, Gwamnan ya kuma bayyana farin cikinsa da wannan ci gabar inda ya kara jadadda goyon bayan gwamnatin Lagos ga al'ammuran wasanni.

Wannan dai shine karon farko da Barcelona ke bude kwallejin da zai mayar da hankali kan horas da ‘yan wasan kwallon kafa a Afrika.

Najeriya na daga cikin kasashen Afrika dake da shahararrun 'yan wasan Kwallo a Duniya, ana kuma da dinbin magoya bayan kungiyar wasan kwallon Barcelona a kasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.