Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi ya ci wa Barcelona kwallaye 425 a wasanni 500

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona, Lionel Messi ya ci wa kungiyarsa kwallaye 425 a wasanni 500 cif cif da ya buga mata.

Lionel Messi na Barcelona
Lionel Messi na Barcelona Reuters/Grigory Dukor
Talla

A jiya ne dai dan wasan ya zura kwallo ta 425 a wasan da Barcelona ta lallasa Real Betis da ci 4-0 a gasar La Liga, lamarin da ya bai wa Barcelona damar dare wa saman teburin gasar da maki 38 yayin da Atletico Madrid ke bi mata da maki 38, sai Real Madrid mai maki 36.

Yanzu haka dai Barcelona ta kammala wasanni a wannan shekarar ta 2015 da kwallaye 180 da ta yi nasarar zura wa a raga.

Itama Real Madrid ta casa Real Sociedad da ci 3-1 a wasan da suka jiya a gasar ta La Liga.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.