Isa ga babban shafi
Wasanni

Leicester da Manchester City sun yi kunnan doki

A jiya talata kungiyoyin kwallon kafa na Leicester da Manchester city sun fafata a gasar Premier ta Ingila, inda suka tashi ba kare bin damo, babu wanda ya ci wani.

Leicester da Manchester City
Leicester da Manchester City youtube.com
Talla

Masu tsaren gida na kungiyoyin biyu sun taka rawar gani, lura da yadda suka hana a zura ko da kwallo guda a raga.

To sai dai dan wasan Leicester Jamie Verdy ya zubar da wata kyakkyawar dama a lokacin da ake dab da tafiya hutun rabin lokaci kamar yadda shi ma Raheem Sterling da Nicolas Otamendi na Manchester City suka zubar da tasu damar.

Yanzu haka dai Leicester na da maki 39 a teburin gasar Premier yayin da ta ke bin Arsenal wadda ke jan ragar teburin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.