Isa ga babban shafi
Wasanni

Kotun Uruguay na tuhumar Figueredo kan cin hanci

Yau ne tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Eugenio Figueredo zai bayyana a gaban kotun kasarsa ta asali wato Uruguay domin fuskantar tuhuma dangane da zarginsa da hannu a badakalar cin hanci da rashawa a FIFA.

Eugenio Figueredo
Eugenio Figueredo
Talla

Figueredo mai shekaru 83 da haiihuwa kuma tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta kudancin Amurka na cikin manyan jami’an FIFA bakwai da jami’an tsaro suka cafke a wani kasaitaccen Otel da ke birnin zurich na kasar Switzerland a watan mayun da ya gabata sakamakon zargin su da aikata laifin cin hanci da rashawa.

Hukumomin Switzerland za su tasa keyarsa a yau Alhamis zuwa Uruguay yayin da ake sa ran jirginsa zai isa kasar da misalin karfe 12 na rana agogon GMT.

Tuni dai masu shigar da kara na gwamnati suka bayyana cewa, akwai yiyuwar Figueredo ya fuskanci hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari matukar aka same shi da aika laifin da ake zarginsa akai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.