Isa ga babban shafi
Wasanni

Van Gaal ya fusata da tambayoyin 'yan jarida

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchster United Louis Van Gaal ya fice daga zauren taron manema labarai cikin fushi da aka gudanar a jiya laraba bayan amsa tambayoyi uku kacal. 

Kocin Manchester United Louis Van Gaal
Kocin Manchester United Louis Van Gaal wsc.co.uk
Talla

Van Gaal mai shekaru 64 da haihuwa bai ji dadin tambayoyin da 'yan jarida suka yi masa ba game da makomarsa a Manchester United yayin da ake ta rade radinn cewa da yiwuwar kungiyar ta raba gari da shi.

An gudanar da taron 'yan jaridan ne gabanin wasan da Manchester United za ta yi a ranar asabar da Stoke City kuma tsawon minti 5 kacal aka shafe a taron kafin Van Gaal ya fice.

Sannan ya ce, shi fa ya halarci taron ne domin amsa tambayoyi dangane da dokokin gasar Premier ta Ingila amma ba akan makomarsa.

Manchester United dai ta yi rashin nasara a wasanni shida da ta yi yayin da ta sha kayi  a wasanni guda uku na baya bayan nan da ta yi  da Wolfsburg da Bournemouth da kuma Norwich.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.