Barcelona ce Zakara a duniya
Barcelona ta lashe kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa da aka kamala a Japan bayan ta doke River Plate ta Argentina ci 3 da 0 a ranar Lahadi.
Wallafawa ranar:
Messi ne ya fara bude raga yayin da kuma Suarez ya jefa kwallaye biyu.
Suarez ne aka zaba gwarzon dan wasa a gasar, bayan ya jefa yawan kwallaye biyar a wasanni biyu.
Lionel Messi ne na biyu da kyautar azurfa sai Andres Iniesta a matsayi na uku.
Barcelona ta kafa tarihi a matsayi kungiya ta farko da ta lashe kofin gasar sau uku. Kuma Messi ya kasance dan wasa na farko da ya zirara kwallaye a wasannin karshe da Barcelona ta buga a gasar cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa.
Kofi na biyar ke nan da Barcelona ta lashe bayan ta lashe kofin zakarun Turai da La liga da Copa del Ray da kofin Super na Turai a kaka guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu