Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona za ta samu euro biliyan1 a shekara

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Josep Maria Bartomeu ya bayyana cewa kungiyar na burin zama wadda ta fi ko wacce kungiyar kwallon kafa a duniya samun kudade.

Josep Maria Bartomeu, shugaban Barcelona.
Josep Maria Bartomeu, shugaban Barcelona. REUTERS/Gustau Nacarino
Talla

Bercelona na bukatar cimma burinta nanda da shekaru shida masu zuwa kamar yadda Bartomeu ya sanar a wata hira da aka yi da shi wadda aka watsa a yau jumma’a.

Shugaban ya ce, Barcelona za ta samu kudin da yakai euro miliyan 600 a wannan shekarar kadai amma ta na sa ran nan da shekara ta 2021 da za ta dinga samun euro biliyan 1 a kowacce shekara.

Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka Real Maddrid da Manchester United ne ke kan gaba a matsayin kungiyoyn kwallon kafa a duniya da suka fi samun riba a bara, inda Real Madrid ta samu euro miliyan 549 yayin da Manchester United ta samu euro miliyan 518.

Barcelona dai ta ce za ta zama kungiya ta farko da za ta fara samun euro biliyan 1 a shekara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.