An yanke hukuncin daurin shekaru uku akan ma'aikatan Aljazeera
A yau asabar ne wata kotu a kasar Masar ta yankewa ma’aikatan tashar talabijin din Aljazeera 3 hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari, saboda samun su da laifin yada labaran karya acewar gwamnatin kasar.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatan sun hada da Mohammed Fahmy dan kasar Canada da Baher Mohammed dan kasar Masar, yayin da Peter Greste, dan Australia ya koma kasar sa.
Tuni dai Kasashen duniya suka nuna rashin amincewarsu tare da yin Allah wadai da hukuncin yayin da Giles Trendle, shugaban gudanarwar tashar ta Aljazeera ya bayyana hukuncin a matsayin bakar rana ga bangaren shari’ar Masar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu