Isa ga babban shafi
Masar

Ma’aikacin Aljazeera dake tsare, zai rasa takardunsa na zama dan kasa

Ma’aikacin tashar talabijin ta Aljazeera mai suna Mohamed Fahmy dan asalin kasar Masar da Canada, ya amince ya rasa takardarsa ta shaidar zama dan kasar Masar kafin sallamar sa daga gidan yari 

cbc.ca
Talla

A kasar Masar jiya litinin ne aka saki Peter Greste, wani ma’aikacin Aljazeera dan kasar Australia karkashin wani kuduri na shugaba Abdulfateh Alsisi.

A dayan bangaren kuwa, Kasar Canada ta bayyana cewa, ba da jimawa ba ne Mohamed Fahmy zai fito daga gidan yari, sai dai ya zuwa yanzu, ba'a san makomar abokin aikinsa da aka tsaresu tare a Shekarar 2013 ba, wato Baher Mohamed.

 

An dai tsaresu ne bisa zargin hada Baki da 'ya'yan Jam'iyyar 'Yan Uwa Musulmi, suna yada bayanan karya bayan da Dakarun kasar sun hambarar da Gwamnatin tsohon shugaban kasar, Mohammed Morsi.

 

Tun a wannan lokacin ne dai kasar Masar ta fada cikin tashin hankali, inda masu hamayya da hukumomin kasar ke ta shirya bore na nuna rashin amincewa da rashin adalcin da suke ganin hukumomin kasar basa yi masu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.