Boko Haram: An haramta sanya Hijabi a Diffa
Hukumomi a jihar Diffa sun sanar da haramta sanya hijabi a duk fadin jihar da ke gabashin Jamhuriyar Nijar yankin da ke fama da ayyukan Boko Haram.
Wallafawa ranar:
Kafafen yada labaran kasar sun jiyo Gwamnan Diffa Yakuba Soumaba Gaoh na cewa, wannan haramci za a ci gaba da yin amfani da shi har sai zuwa lokacin da aka samu narasar kakkabe ayyukan Boko Haram baki daya a yankin.
A makwannin da suka gabata, kasar Chadi ta dauki irin wannan mataki na hana sanya Hijabi da kuma shiga kasuwanni a fadin kasar domin kwace Hijabin daga ‘yan kasuwa, aka kona baki daya, saboda barazanar Boko Haram.
Rikicin Boko Haram na Najeriya dai ya shafi Nijar da Chadi da Kamaru, inda suke ci gaba da kai hare hare a kasashe da ke kewaye da tafkin Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu