Isa ga babban shafi
Najeriya

Yadda Sojojin Najeriya suka kwato Dikwa daga hannun Boko Haram

Rundunar sojan Nigeria ta 7 da ke Maiduguri ta ce dakarun kasar sun kwato garin Dikwa da ke jihar Borno, bayan da garin ya share watanni da dama a hannun ‘yan kungiyar boko haram

Dakaron Najeriya sun kwato Dikwa tare da kwato muggan makamai daga hannun Boko Haram
Dakaron Najeriya sun kwato Dikwa tare da kwato muggan makamai daga hannun Boko Haram dailypost.ng
Talla

A ranar 23 ga watan Yuli ne dakarun Najeriya suka shiga Dikwa, kuma a ranar Juma’a ne rundunar Sojin kasar ta sanar da kwato ikon garin daga hannun Mayakan Boko Haram.

Mataimakin daraktan sashen yada labarai na rundunar sojojin kasar a Maiduguri Kanal Tukur Gusau, ya shaidawa wakilin RFI Hausa Bilyamin Yusuf cewa sun tarwatsa Boko Haram tare da kashe mayaka 20

Gusau ya ce sun kwato manyan makamai da Bindigogi da suka hada da wadanda ke iya kakkabo jirgin sama, sannan sun lalata motocin Boko Haram da dama.

Gusau ya kara da cewa za su tatsi bayanai daga wasu layukan saluka guda hudu da suka samu daga mayakan na Boko Haram.

01:32

Kanal Tukur Gusau

Bilyaminu Yusuf

Sojojin kasa da sama ne na Najeriya suka kwato Dikwa inda suka tarwatsa sansanin da mayakan Boko Haram ke fake wa domin kai harin kwantar bauna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.