Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisa : APC ta yi watsi da zaben Saraki da Dogara

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi watsi da zaben shugabannin Majalisar Tarayya inda aka zabi Bukola Saraki a matsayin shugaban Majalisar Dattijai da Yakubu Dogara a matsayin Kakakin Majalisar Wakilai.

Bukola Saraki ne Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya
Bukola Saraki ne Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

APC ta yi watsi da zaben shugabannin Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Jam’iyyar tace ba da yawunta aka zabi Saraki da Dogara ba domin mambobinta ba su ra’ayin shugabancinsu.

Jam’iyyar da ke da rinjaye a zauren Majalisun guda biyu ta ce zaben gwaji da ta gudanar ya nuna wadanda ya kamata su jagoranci Majalisar.

Lai Muhammed, Kakakin APC wanda ya sanya wa sanarwar hannu ya ce bukatun jam’iyyar ya rinjayi na wasu tsiraru.

Ya kuma ce shugabannin Jam’iyyar za su tattauna domin daukar mataki akan wasu ‘yayan Jam’iyyar da suka bijerewa bukatunta.

Bayan an rantsar da Bukola Saraki a matsayin sabon shugaban Majalisa ta 8, ya yi alkawalin gudanar da jagoranci na gaskiya tare da godewa wadanda suka amince da jagorancinsa.

Senata Shehu Sani na APC mai wakiltar Kaduna wanda ya kauracewa Majalisar, ya ce Shugaban kasa muhammadu Buhari zai fuskanci kalubale wajen cim ma bukatun APC na tabbatar da canji a Najeriya saboda tasirin PDP a shugabancin Majalisun Tarayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.