Isa ga babban shafi
Najeriya

APC ta zabi 'yan takara a neman shugabancin Majalisar Dattawa

A cikin daren jiya daren jiya asabar ‘yan majalisar dattawa daga jam’iyyar APC a Najeriya, sun zabi Sanata Ahmed Lawal daga jihar Yobe da kuma George Akume daga jihar Benue a matsayin ‘yan takarar jam’iyyar a zaben shugaba da kuma mataimakin shugaban majalsiar dattawan da ake shirin gudanarwa a ranar talata.

Tambarin jam'iyyar APC a Najeriya
Tambarin jam'iyyar APC a Najeriya
Talla

APC jam’iyyar da ta kafa gwamnati a matakin tarayya, tana da wakilai 59 daga cikin 109 a zauren majalisar dattawan.

Bayan share tsawon yinin jiya, sai a cikin dare ne ‘yan majalisar na APC suka cimma matsaya a game da wadanda za su tsaya masu takarar, to sai dai kamar yadda bayanai ke nunawa, sauran ‘yan majalisar dattawa da ke biyayya ga daya dan takarar sanata Bukola Saraki daga jihar Kwara sun kaurace wa zaben.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.