Isa ga babban shafi
Najeriya

APC ta yi watsi da kalaman Jonathan akan Buhari

Jam’iyyar APC mai jiran karbar ragamar shugabanci a kasar ta yi watsi da kalaman Shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan game da zargin da ya yi cewa yana tausayawa Ministocinsa idan Buhari ya karbi mulki domin za’a kuntata musu.kakakin yakin neman zaben Janar Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya shaidawa Radio France internatonale cewa, kawai rudewa ce irin na Shugaban mai barin gado na barin karagar mulki.

Shugaban Najeriya mai Jiran Gado, Janar Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya mai Jiran Gado, Janar Muhammadu Buhari AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Ajiya lahadi ne dai Shugaba Jonathan, yayin bikin ban-kwana da mulki a wani coci da ke  babban birnin kasar na Abuja, ya ce, "Ina tausaya wa ministocina da masu ba ni shawara saboda za a gallaza muku. Don haka dole ne ku shirya domin fuskantar abin da zai biyo baya".

Goodluck Jonathan, ya kuma bayyana yadda abokansa da sauran makusantansa suka guje shi tun bayan shan kayen da ya yi a zaben shugaban kasar da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.