Isa ga babban shafi
Wasanni

Babu tabbacin ranar da Bale zai dawo wasa - Zidane

Mai horar da kungiyar Real Madrid Zineden Zidane ya ce babu taka-maiman lokacin da dan wasansa Gareth bale zai dawo buga wasa, abinda ke nufin ba zai haska ba a fafatawar da Madrid din zata yi da kungiyar Tottenham a gasar zakarun nahiyar turai.

Gareth Bale na kungiyar Real Madrid yayin kokarin jefa kwallo a ragar kungiyar Borussia Dortmund, a fafatawar da suka yi da gasar Zakarun kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai.
Gareth Bale na kungiyar Real Madrid yayin kokarin jefa kwallo a ragar kungiyar Borussia Dortmund, a fafatawar da suka yi da gasar Zakarun kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai. REUTERS/Wolfgang Rattay
Talla

Tun a wasan gasar zakarun turan da Madrid doke Borussia Dortmund ne Bale ya samu rauni, hakan ya sabbaba rashin buga wasa da kasarsa ta Wale ta buga, na neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya, wanda suka gaza samun nasarar samun cancantar.

To sai dai a gefe guda dan wasa mai tsaron baya na Madrid Dani Carvajal da aka gano ya kamu da cutar zuciya a makwannin da suka gabata ya dawo atasaye.

Mai horar da Madrid Zidane, ya ce zuwa yanzu dukkanin gwaje-gwajen da likitoci suka yi wa Carvajal na nuni da cewar yana samun lafiya.

A ranar Lahadi mai zuwa Real Madrid zata fafata da kungiyar Girona a gasar la liga, kafin daga bisani su yi tattaki zuwa Ingila domin fafatawa da kungiyar Tottenham a cigaba da gasar kwallon kafa ta zakarun nahiyar Turai, a ranar Laraba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.