Isa ga babban shafi
wasanni

Kofin kwallon kafa na zakarun nahiyar Afrika

A jiya lahadi ne aka buga wasannin gaf da na karshe a gasar neman kofin kalubale na nahiyar. A filin wasa na Rades da ke Tunisa, Club Africain na Tunisia ya sha kashi a hannun Supers Sport United na Afirka ta Kudu ci 3-1.

'Yan wasan TP Mazembe na murnar cin kofin zakarun nahiyar Afrika a birnin Lubumbashi.
'Yan wasan TP Mazembe na murnar cin kofin zakarun nahiyar Afrika a birnin Lubumbashi. STRINGER / AFP
Talla

A birnin Rabat na Maroko an tashi canjaras tsakanin FUS Rabat da TP Mazembe na Jamhuriyar dimokuradiyya Congo. To amma duk da haka TPM mezembe ce ta yi nasara zuwa zagayen karshe saboda nasarar da ta yi a wasan da suka yi a zafayen farko.

Za a yi karawar karshe domin daukar kofin ne tsakanin TP Mazembe da Super Sport United, inda za a kara har sau biyu, da farko a birnin Lubumbashi na Congo a ranar19 ga watan  nuwamba, sai kuma zagaye na biyu a ranar 24 ga watan nuwambar a Afrika ta Kudu. Duk wanda ya yi nasara za a ba shi tukuicin dala milyan daya da dubu 250.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.