Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya sallami jami'en da suka gabatar da shaidu yayin tsige shi

Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami biyu daga cikin mahimman mutanen da suka gabatar da shaidu yayin zaman bin bahasin tsige shi, lamarin da ya janyo zargin cewa shugaban ya fara aiwatar da kudirin ramuwar gayya.

shugaban Amurka Donald Trump.
shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Leah Millis
Talla

Shugaba Trump ya yi wa jakadan Amurka a Tarayyar Turai, Gordon Sondland, kiranye, sa’o’i bayan ya umurci hafsan sojin nan mai aiki a fadar White House Kanar Alexander Vindman da ya bar fadar.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan majalisar dattawar kasar ta wanke shi daga zargin yin amfani da mukaminsa wajen aikata ba daidai ba.

Sondland, wanda aka nada kan mukamin bayan ya bada gudummawar dala miliyan daya yayin rantsar da shugaba Trump ya ce an shaida mai za a sallame shi daga mukamin na sa.

Shi ma Vindman, jami’in soji mai kima, wanda ya taba samun rauni a Iraki, an sallame shi ne nan take, aka kuma umurce shi da ya bar ofishinsa na fadar White House ba tare da bata lokaci ba.

Lauyan Vindman, David Pressman ya ce duk da yadda hafsan sojin ya yi wa kasarsa bauta tsakani da Allah, rako shi aka yi har wajen fadar White House ‘soboda ya fadi gaskiya’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.