Isa ga babban shafi
Amurka

Pelosi ta kekketa takardar Trump a gabansa

Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kekketa takardar jawabin shugaba Donald Trump bayan ya kammala jawabinsa kan halin da kasa ke ciki a zauren majalisar kasar.

Lokacin da Nancy Pelosi ke kekketa takardar jawabin shugaban Amurka Donald Trump
Lokacin da Nancy Pelosi ke kekketa takardar jawabin shugaban Amurka Donald Trump politico
Talla

A karon farko shugaba Trump ya ki musafaha da shugabar Majalisar duk da cewa ta mika masa hannu amma ya yi watsi da ita, abin da ake kallo a matsayin daya daga cikin dalilan da suka harzuka ta har ta kekketa takardarsa a idon duniya.

A yayin jawabin nasa na tsawon mintina 80, shugaba Trump ya kauce wa batun dambarwar tsige shi daga karagar mulki.

Trump ya kuma tabo batutuwan da suka hada da yake-yaken Amurka a wasu kasashen duniya da shirin janye dakarun kasar daga Afghanistan da muhimmancin Amurka a duniya da kuma hallaka kwamandan Iran Qaseem Souleimani.

Shugaban ya sha alwashin hallaka duk wanda ya kai hari kan wani Ba'amurke da kuma kawo karshen mulkin kama-karya da ke gudana a Venezuela a karkashin Nicolas Maduro wanda ya ce, yana samun goyan bayan kasashen Rasha da China da kuma Cuba.

Trump ya kuma kambama Amurka a matsayin kasar ‘yanci wadda ta samar da daidaito da kuma cika burint.

A cewar Trump, "Amurkawa ne ke sahun gaba,mun kafa sabuwar duniya, kuma muna sauya tarihi".

A wannan Larabar ake sa ran Majalisar Dattawan Amurkar wadda jam'iyyar Republican ke da rinjaye a cikinta, ta wanke shugaban daga zargin da ake yi masa na yin amfani da karfin ikonsa ta hanyara da ba ta dace ba.

Tuni Majalisar Wakilai mai rinjayen Democrat ta tsige shugaban daga karagar mulkinsa, yayin da take dakon matakin da Majalisar Dattawa za ta dauka kan lamarin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.