Isa ga babban shafi
Birtaniya

Julian Assange mai shafin Wikileaks zai shafe shekara 1 a yarin Birtaniya

Kotu a Birtaniya ta aike da mamallakin shafin Wikileaks mai kwarmata asirin gwamnatocin duniya Julian Assange gidan yari na makwanni 50 bayan samunsa da laifin karya sharuddan belin da aka bashi a shekarar 2012, inda ya yi zaman gudun hijirar shekaru 7 a Ofishin jakadancin Ecuador don gujewa aika shi Sweden don fuskantar hukunci.

Julian Assange mamallakin shafin Wikileaks
Julian Assange mamallakin shafin Wikileaks REUTERS/Henry Nicholls
Talla

Julian Assange wanda aka kama shi a ranar 11 ga watan Aprilun da ya gabata bayan da Ecuador ta dauki matakin mika shi, yanzu haka zai shafe wa’adin na shekara guda babu mako biyu a gidan Yari.

Akwai dai bayanai da ke nuna cewa bayan Assange mai shekaru 47 ya kammala wa’adinsa na shekara guda a gidan yarin Birtaniya, kai tsaye za a mika shi ga Amurka don fuskantar hukunci kan bankada wasu bayanan sirrin kasar ga duniya da shafinsa na Wikileaks ya yi shura akai.

Yayin da Assange ke fitowa daga harabar kotun da aka yanke masa hukuncin an ga yadda magoya bayansa, suka riga kuwwa tare da fadar maganganu marasa dadi ga jami’an tsaron kasar.

Wasu daga cikin bayanan sirrin da shafin na Wikileaks mallakin Assange ya kwarmata kuma ya ke jiran hukuncin kan su a bangaren akwai badakalar da sojin Amurka ke tafkawa a Iraqi batun da Assange ya hada hannu da wani tsohon jami’in leken asirin Amurka wajen samun bayanai, wanda sanadiyyarsa ne Amurka ke nemanshi don yi masa hukunci.

A bangaren kashin kansa kuwa akwai laifuka masu alaka da cin zarafin mata da kuma fayde a Sweden batun da shima ya ke jiran hukunci kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.