Isa ga babban shafi
Ecuardo

Ecuador za ta cigaba da tattaunawa da Birtaniya akan Assange a wannan satin

Kasar Ecuador ta ce za ta cigaba da tattaunawa da kasar Birtaniya akan makomar mai wallafa bayanan sirri a shafin yanar gizo, Julian Assange a wannan satin.Ministan harkokin wajen kasar Ecuador, Ricardo Patino, a cewar gidan telebijin kasar, ya ce za a fara tattaunawar bayan kasar Birtaniya ta ce tana da niyyar komawa kan teburin tattaunawa.  

Mai wallafa bayanan sirri a shafin yanar gizo, Julian Assange.
Mai wallafa bayanan sirri a shafin yanar gizo, Julian Assange. REUTERS/Andrew Winning
Talla

Assange dai ya sami mafaka ne a ofishin jakadancin kasar Ecuador da ke Birtaniya tun a watan Yuni bana, bayan ya kasa samun rangwamen daga kotu da kada a tisa keyarsa zuwa kasar Sweden inda ake zarginsa da yin fyade.

Assange dai ya na gudun kada a mika shi ne ga kasar Amurka idan ya bar ofishin jakadancin na Ecuador.

A watan jiya ne, kasar ta Ecuador ta ba Assange mafakar siyasa, inda kasar ta Birtaniya, ta dauki alwashin sai ta kama shi idan ya fito.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.