Isa ga babban shafi

Bakin-hauren da Italiya ta kora sun isa Spain

Jiragin ruwan Aquarius mai dauke da bakin-haure 630, da Italiya da haramtawa shiga cikinta, ya isa tashar ruwan birnin Valancia da ke Spain da safiyar yau Lahadi.

Bakin-haure yayin da suke sauka daga jirgin ruwan ceto Aquarius, a lokacin da ya isa tashar jiragen ruwa ta Valencia, Spain.
Bakin-haure yayin da suke sauka daga jirgin ruwan ceto Aquarius, a lokacin da ya isa tashar jiragen ruwa ta Valencia, Spain. REUTERS/Heino Kalis
Talla

A makon da ya gabata ne Spain ta bayyana aniyar taimakawa bakin-hauren mafi akasari da suka fito daga nahiyar Afrika, bayanda Italiya ta hana su isa gabar ruwanta.

Daga cikin bakin hauren akwai mata masu juna biyu 7 da kuma kananan yara 123.

Yawan bakin-hauren da Spain ke karba na ci gaba da karuwa, bayan da a wani aikin ceto da jami’an gabar ruwan kasar suka gudanar, tsakanin ranar Juma’a da Asabar, suka ceto wasu bakin-hauren 933 daga hallaka a tekun Mediterranean.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.