Isa ga babban shafi

Jami'an tsaron Spain sun ceto bakin-haure 933 daga teku

Jami’an tsaron bakin Teku na Spain, sun ceto wasu bakin-haure 933, tare da tsamo gawarwakin wasu 4 daga tekun Mediterranean a tsakanin jiya Juma’a zuwa yau Asabar.

Wasu daga cikin bakin-hauren da sukai kokarin ketara tekun Mediterranean zuwa nahiyar turai.
Wasu daga cikin bakin-hauren da sukai kokarin ketara tekun Mediterranean zuwa nahiyar turai. Reuters
Talla

Aikin ceton ya gudana na a yankin tekun na Meditteranean da ke tsakanin arewa maso gabashin Morocco da kudu maso gabashin Spain.

Lamarin ya faru ne dai dai lokacin da kasar ta Spain ke shirin karbar wasu bakin haure 629 da kasashen Italiya da Matlta suka ki karba.

Kididdigar da hukumar lura da iyakokin kungiyar kasashen turai, ta nuna cewa akwai yiwuwar a samu karin yawan bakin-hauren da ke tserewa zuwa Spain don gujewa fatara da yaki daga wasu kasashe masu tasowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.