Isa ga babban shafi
Amurka

Dokar haramtawa baki Musulmi shiga Amurka zata fara aiki

Kotun Kolin Amurka ta bai wa shugaba Donald Trump damar aiwatar da wani bangare na dokar haramta wa wasu kasashen musulmi shiga cikin kasar.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Matakin kotun yana a matsayin nasara ga Trump, wanda ya sha nanata cewa, dokar tana da muhimmanci don kare kasar daga barazanar ta’addanci.

Jim kadan da yake hukuncin Kotun Kolin kasar ta Amurka, shugaba Donald Trump ya ce, hukuncin ya bada damar haramta wa ‘yan kasashen Musulmin shida da ka iya brazanar ta’addanci ga Amurka, shiga kasar.

Trump ya ce, a matsayinsa na shugaban kasa, ba zai amince wa wasu mutane da ka iya cutar da Amurka ba.

Kotun kolin ta ce, dokar wadda wata karamar kotu ta soke ta a can baya, za a iya amfani da ita har na tsawon kwanaki 90, wajen dakatar da mutanen wadannan kasashe shida da ba su da alaka da wani a Amurka.

Har ila ya dokar ta amince a dakatar da ‘yan gudun hijira har na tsawon kwanaki 120 daga shiga Amurkan.

Dokar dai za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar da alkalan kotun kolin za su sake gudanar da wani zama a cikin watan Oktoba mai zuwa don nazari kan yiwuwar bai wa dokar dukkanin goyon-baya ko kuma akasin haka.

Kasashen da dokar ta shafa, sun hada da Iran, Libya, Somalia, Sudan, Syria da kuma Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.