Isa ga babban shafi
Amurka

''Ba a Mun adalci''

Shugaba Donald Trump da ke fuskantar kalubale ya ce a tarihin kasar ba a taba yin wani shugaba da aka nunawa rashin adalci ba kamarsa.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ana nuna masa rashin adalci
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ana nuna masa rashin adalci 路透社
Talla

Wannan na zuwa a yayin da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyarsa ta Republican a majalisar dokoki suka bukaci hujjoji daga zarge-zargen da ake wa shugaban.

A lokacin da ya ke jawabi a wani bikin ya’ye jami’an tsaron teku, Mista Trump ya ce ana nuna masa rashin adalci karara kuma ba zai taba yadda a ga bayansa ba.

A jiya an shafe lokaci Trump bai ce komai ba a Twitter, hanyar da ya saba mayar da martani ko tsokaci kan batutuwan da suka shafi gwamnatinsa.

Fadar white house ta fuskanci jerin zarge-zarge da ke zuwa daya bayan daya, kuma babban muhimmin batu shi ne kan zargin Trump ya bukaci FBI ta daktar da binciken daya daga cikin masu ba shi shawara.

Da kuma zargin ya yi musayar wasu manyan bayanan sirrin Amurka da Rasha.

Amma a lokacin da ya ke mayar da martani, kakakin Majalisar dokoki Paul Ryan ya ce babu shakka akwai wadanda ke yi wa shugaban zagon kasa.

Mista Ryan ya ce za su ci gaba da gudanar da nasu binciken ba tare da nuna wani banbancin jam’iyyar da ke kan mulki ba.

Yanzu haka dai wasu ‘yan Republican sun fara hada kai da ‘yan Democrat a Majalisa domin ganin an gudanar da bincike kan zargin alakar gwamnatin Trump da Rasha.

Tuni dai aka nada wani tsohon shugaban hukumar leken asiri ta FBI Robert Mueller dan jagorancin binciken.

Mataimakin Babban lauyan gwamnatin kasar Rod Rosenstein ya ce ganin muhimmancin binciken da kuma yadda jama’a ke bukatar sanin gaskiyar abinda ya faru, ya sa aka zabo Mueller.

A martanin da ya mayar cikin gaggawa, shugaba Trump ya ce babu wani sabon abinda basu sani ba da binciken zai haifar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.